TASKAR BABAN SALMA

Babu wata al'uma ingantatta wadda bata da tarihin ta! daga Taskar Baban Salma

Abubuwa 13 daya kamata kusani game da nahiyar Afrika

Wallafan May 22, 2020. 10:28pm. Na Abubakar A Gwanki. A Sashin Dauloli

http://zamaniweb.com/administrator/files/20/05/168/map_of_afrika.jpg
- Afrika kyakkyawar nahiya ce mai Arziki da al’adu daban-daban wanda ya bambanta ta cikin nahiyoyi 7 na duniya

- Afrika nata albarkatu masu yawa, da kuma abubuwan sha’awa masu daukar hankali na shakatawa


- Afrika itace nahiya ta biyu a bangaren girma cikin nahiyoyin duniya kuma itace ta biyu a bangaren yawan mutane a nahiyoyin duniya

Abubuwa 13 da ya kamata ku sani game da Nahiyarku ta Afirka


 1. Afrika kwakkyawar nahiya ce mai Arziki da al’adu daban-daban wanda suka bambanta ta cikin cibiyoyi 7 na duniya.
 2. Afrika na da albarkatu masu yawa, da kuma abubuwa masu daukar hankali na shakatawa. Zagaye da binciken nahiyar zai bayyana abubuwan sha’awa game da Afrika
 3. Afrika ta kasance itace nahiya ta biyu bangaren girma cikin nahiyoyin duniya, kuma itace ta biyu ta bangaren yawan mutane a nahiyoyin duniya
 4. Tana da fadin kilomita saqwaya miliyan 30.3 da tsawo na tsibirai, watau ta mamaye kashi 6 na fadin duniya.
 5. Itace mai kashi 20 na yawan kasar duniya.
 6. Afrika ta yaye ne daga hannun Turawan mulkin mallaka, banda kasar Itopiya (Habasha) da kasar Liberiya.
 7. Afrika ce ta biyu na yawan mutane, inda take dauke da mutane a kalla Biliyan 1.1 ko ace kashi 16 na yawan mutanen duniya
 8. Ba'a fiye samun girgizar kasa a Nahiyar ba.
 9. An wawashe jama'arta da arzikinta lokutan cinikin bayi da na mulkin mallaka. Kuma har yanzu arewacin nahiyar a hamadar Sahara yana hannun Larabawa ne.
 10. Har yanzu nahiyar ita ce ta karshe wajen ci gaba da aiki da kwakwalwa.
 11. Yakin duniiya na daya da na biyu bai shaffe ta sosai ba.
 12. A nan ne aka fi ganin tsoffin kasusuwan dan-Adam, wanda hakan ya nuna a nan ne mutane suka fara bulla.
 13. Da yawan kasashen dattijai da tun mulkin mallaka suke gwamnati, su da iyalansu ke mulki a nahiyar, musamman mulkin kama-karya.

Tura wannan zuwa:

An yi sharhi 1 a kan "Abubuwa 13 daya kamata kusani game da nahiyar Afrika"


Babu hoto16-01-2021
Abbas bello

lalle nahiyarmu ta africa cike take da ababen mamaki tun da dadewa,allah yakara bamu zaman lafiya da ci gaba me dorewa a naihiyarmu ta africa.

Wallafa Sharhi

Suna:

Adireshin Email:

Sharhin:

Taskar Baban Salama, Taskar Tarihi

Barka da zuwa Taskar Baban SalmarnrnWannan dandali ne matattarar tarihi, wadda zata rinka kawo bayanai dangane da tarihi kan abubuwan da suka shude cikin harshen hausa. Abubakar A Gwanki ne babban mai gudanarwa a shafin. Kasantuwar sa mai sha'awa da tarihi ne kuma mai yawan karance karancen tarihi, shiyasa shima ya bude wannan farfajiyar domin samar da makaloli wadanda suka danganci tarihi cikin harshen Hausa.


Abubakar A Gwanki

Abubakar A Gwanki ne mai gudanarwa kuma mawallafin dukkannin abubuwan da wannan shafin ya kunsa.
Abubakar A Gwanki, masoyin tarihi ne sosai, kuma yana da sha'awar yin karance karance musamman na abubuwan da suka danganci tarihi.


Kasidu Masu Alaka