TASKAR BABAN SALMA

Babu wata al'uma ingantatta wadda bata da tarihin ta! daga Taskar Baban Salma

Abubuwa goma da musulmai ne suka kirkire su

Wallafan May 21, 2020. 6:51pm. Na Abubakar A Gwanki. A Sashin Fannin Kirkira

Hada da jami'ar farko da burushin goge hakora, akwai abubuwan mamaki da yawa wadanda musulmai ne suka kirkire su kuma abubuwan suka sauya fasalin rayuwa a duniya. Anan mun jero abubuwa muhimmai guda goma wadanda musulma ne suka kirkiro su. Mun samu wannan jerin ne daya wani littafi da aka lisafta makirkira guda1001 maisuna 1001 Inventions
1.Kofi (Coffee)
http://zamaniweb.com/administrator/files/20/05/168/coffe.png

Shekaru aru aru da suka wuce a baya, mutane da dama sunyi kokarin samar da wani abu mai muhimmanci wanda mutane zasu rinka sha domin wattsakewa. Sai aka samu wani balarabe mai suna Khaled, ya samowa duniya wannan hanya mai sauki ta ruwan Coffee.


2.Agogo
http://zamaniweb.com/administrator/files/20/05/168/agogo.png
Wani mutum mai dabara maisuna Al-Jazari garin Diyarbakir a kudu maso gabashin Turkiya shine ya fara kirkirar dabarar da ta samar da agogo. Yazuwa shekarar 1206, Al-jazari ya samar da ire ire na agoguna da dama. Kasantuwar muna da bukatar wani abu domin gane lokaci, sai gashi mun samu musulmi wanda y kirkiro mana agogo.
Daganan sai mutane suka fara yin amfani dashi wajen tantance lokuta. A haka al'amarin ya dinga juyawa anata sarrafa agogo lokaci zuwa lokaci har kawo ga wannan zamanin.
3.Kyamara
http://zamaniweb.com/administrator/files/20/05/168/kyamara.png

Ta hanyar yin amfani da daki mai duhu, tare da fitar da kofar shigar haske ne Ibn al-Haitham ya samar da abinda yake kira "Qamara", daga nan akasamu kalamar " Camera" a turanci da kuma Kyamara a Hausa. Al-Haitham yayi ta sarrafa wannna dabarar tashi inda tazama dabarar daukar hoto na Kyamara. Dabarar tasa tasha banbam da dabarar Girkawa ta amfani da hasken ido domin Samar da Kyamara din. Dukda yake dai Girkawan sunyi kokari amma saidai dabarar tasu ta gaza.


4.Tsarin tsafta da Sabulu
Saboda addinin musulunci addini ne na tsafta, hakane yasa tun musulman baya sukayi ta kojarin samar da guraren da zasu sauwaka ma mutane alwala da tsaftace jikkunan su. Anan ma mai fasaha Al-jazari ya rubuta littafi wanda ya koyar da yadda aka hada famfo da an matsa sai ruwa ya fito.
Shima Al-Kindi a littafin sa maisuna “Book of the Chemistry of Perfume and Distillations”, ya koyar da yadda ake hada sabulai da turaruka domin tsafta.
5. Burtsatse mai amfani da iska (windmill)

http://zamaniweb.com/administrator/files/20/05/168/screenshot_2020-05-22-13-06-45-1.png Kowacce shekara, bayan daukewar ruwan sama hamada kan bushe ta kone yazamo babu ruwa a sahara. Larabawa sunyita yin dabaru domin samar da ruwa cikin sauki a yankunan su na sahara. A shekarar 634, wani musulmi mai basira ya kirkuro hanyar yin amfani da iska domin samar da ruwa wato Windmill wanda muke gani a halin yanzu.
Windmill na farko yana dauke da fukafukai shida ko goma sha biyu. Suna amfani dashi wajen Samar da ruwan sha dana noman rani. Wannan fasahar ta baiyana a kasashen Turai ne bayan shekaru 500 da samuwar sa a kasashen larabawa.

6. Jirgin sama

http://zamaniweb.com/administrator/files/20/05/168/jirgi.png

Abbas ibn Firnas shine mutum na farko da ya kirkiri abu wanda zai iya daukar mutum ya tashi dashi sama kamar jirgi. A karbi na 9 ya kirkiri abu mai fukafukai wanda yake kama da na tsuntsaye. A garin Cordoba na kasar Spain ya hada abun kuma ya tashi dashi sama, kafinnan ya dan zagaya sannan kuma ya fado kasa yayi sanadiyyar karyewar kashin bayan sa. Komadai yane, mutum na farko da yayi sanadiyyar samuwar jirgin sama na yanz. Wannan fasahar tasa ce tayi sanadiyyar jan hankalin makirkiri dan Italiya Leonardo da Vinci Shekaru dari shida da suka shude.

7. Asibiti da kayan asibiti na zamani

http://zamaniweb.com/administrator/files/20/05/168/asibiti.png

Idan muka koma baya a karni na goma, zamu yi duba zuwa ga malamin asibitinnan Abul Qasim Khalaf ibn al-Abbad al-Zahrawi, mutumin da turawa ke kira da Abulcasis. Ya rubuta littafin insakulofidiya na likitanci. Wannan aiki nasa ne ya samar da sama da kayaiyakin asibiti 200. Wannan aikin nasa ne ya samar da kayaiyakin asibiti na yanzu wanda muke tunanin turawa ne suka kirkiro shi.

8.Taswira

http://zamaniweb.com/administrator/files/20/05/168/map.png
Sama da shekaru 3,500 ake amfani da taswira, saidai kuma irin wannan taswirar ta wannan zamanin wadda ake zanawa a takarda asalinta musulmai ne suka fara gano ta. Saboda musulmai daga sassa duniya na da bukatar tafiya zuwa aikin Hajji domin Sauke daya daga cikin farillai na addinin su, sai suka fara dabarar yadda zasu tafi garin Makka kai tsaye ba tare da wahala ba. Idan suka tafi suna wuce gurare da garuru sai suke zanawa a takarda tare da basu suna tun a karni na bakwai.

9.Rubutaccen kida

http://zamaniweb.com/administrator/files/20/05/168/kida.png

Ko kasan salon kida na zamani wanda ake rubutawa a takarda ko a na'ura mai kwakwalwa ya samo asali sa ne daga Al-Kindi a karni na tara?
Wannan salon da ake kira Solmization kokuma doh, ray, me, far, so, la, tee, da Haruffan larabci na kuma Dal, Ra, Mim, Fa, Sad, Lam, Sin.


10.Algebra

http://zamaniweb.com/administrator/files/20/05/168/algebra.png

Kalmar Aljebra ta samo asalinta ne daga sunan wani musulmi bafarishe malamin ilimin lissafi na karn na tara maisuna Al-Khwarizimi, wanda ya rubuta littafin lissafi na “Kitab al-Jabr Wa l-Mugabala” wanda turawa suka fassara shi zuwa sunan “The Book of Reasoning and Balancing”. Al-Khwarizmi ne ya kirkiro asalin lissafin Algebra.

Tura wannan zuwa:

An yi sharhi 1 a kan "Abubuwa goma da musulmai ne suka kirkire su"


Babu hoto16-01-2021
Abbas bello

alhamdu lillah,wannan yanunama turawan yammacin duniya cewa basu sukafi kowa kimiyyaba, kuma kalu bale garemu musulmi. mutashi tsaye muyi karatu kuma muyi bincike mai zurfi akan 'al amurra, musamman bangaren kimiyya shi zai bamu damar shiga ayi gogayya damu takowane fanni.

Wallafa Sharhi

Suna:

Adireshin Email:

Sharhin:

Taskar Baban Salama, Taskar Tarihi

Barka da zuwa Taskar Baban SalmarnrnWannan dandali ne matattarar tarihi, wadda zata rinka kawo bayanai dangane da tarihi kan abubuwan da suka shude cikin harshen hausa. Abubakar A Gwanki ne babban mai gudanarwa a shafin. Kasantuwar sa mai sha'awa da tarihi ne kuma mai yawan karance karancen tarihi, shiyasa shima ya bude wannan farfajiyar domin samar da makaloli wadanda suka danganci tarihi cikin harshen Hausa.


Abubakar A Gwanki

Abubakar A Gwanki ne mai gudanarwa kuma mawallafin dukkannin abubuwan da wannan shafin ya kunsa.
Abubakar A Gwanki, masoyin tarihi ne sosai, kuma yana da sha'awar yin karance karance musamman na abubuwan da suka danganci tarihi.


Kasidu Masu Alaka