
Ba kamar yadda ake yayatawa ba, tun a shekarun 1300 ake yin mulkin sarauta a nahiyar Afirka, wannan ya sanya ya kamaci duk wani dan Afirka ya dinga gudanar da bincike don sanin sahihin tarihin sa, ba kawai abinda turawa ke fada musu ba.
Alhaji Musa Keita shine mutumin da tarihi ya nuna cewar yafi kowa arziki a duniya, an fi sanin Musa Keita da lakabin Mansa Musa, ma’ana Sarki Musa.
Mansa musa shine Sarki na goma a jerin sarakunan masarautar Mali, kuma yana da arzikin da a yanzu darajarta ta haura dala biliyan 400 ($400bn).

usa Keita na I ya hau kan karagar mulkin kasar Mali a shekarar 1312. Lokacin da aka nada shi, an bashi suna Mansa, ma’ana Sarki. An ce Mansa Musa ya ci birane 24 da yaki, kowannensu yana da gundumomi da suka kunshi manyan garuruwa da kadarori.
Mansa Musa ya shugabanci kasashe da yawa. A takaice ya mulki dukkan (ko sassa) na Mauritania, Senegal, Gambiya, Guinea, Burkina Faso, Mali, Niger, Nigeria, da Chadi.
Dukiyarsa ta shahara a duniya a lokacin da ya tafi aikin Hajji a shekarar 1324 zuwa garin Makka, wanda ya yi tafiya mai nisan mil 4000.
An samu labarin cewa yana da kadarori da suka haɗa da mutane 60,000, ciki har da bayi 12,000 waɗanda kowannensu yana daukar sandunan zinare mai nauyin kilo 4, haka kuma suke shirya dawakai da jakuna.
Musa ya samar da dukkanin abubuwan bukata domin ya ciyar da gaba daya mutanen sa da dabbobinsa. Wadannan dabbobi sun hada da rakuma 80 wadanda kowannensu yake daukar kaya mai nauyin kilogiram 50 zuwa 300.
Musa na bawa talakawa zinarin da ya hadu da su ta hanyar sa. Ba wai kuma kawai ya na kyauta a biranen da ya bi ta kan hanyar zuwa Makka ba ne, ciki har da birnin Alkahira da Madina, An ruwaito cewa yana gina Masallaci a ranar kowacce Juma’a.
Musa ya lalata tattalin arzikin yankunan da ya ratsa ta wadanda suka hada da biranen Alkahira, Madina, da Makka, Darajar zinare ta lalace har a shekaru masu zuwa. Farashin kayayyaki sun fadi a wadannan birane. Don daidaita kasuwar zinare, a hanyarsa ta dawowa daga Makka, Musa yana karbar duk wani zinare da zai iya karba daga masu bada bashi a Alkahira, da kudin ruwa mai yawa.
Tarihi ya nuna cewa wannan ne karo na farko da wani mutum ya daidai ta farashin gwal a kasuwannin duniya.
Bayan ya yi sarauta ta tsawon shekaru 25, Mansa Musa ya mutu a shekara ta 1337. Sai dan sa mai suna Maghan na I ya gāji sarautarsa ta kasar Mali.
A zamanin sa, Mansa Musa ya ci masarautu 24 da yaki, wadanda ya mamaye su da karfin mulkinsa kuma ya hade su a masarautar sa. Masana tarihi da dama sun bayyana shakkun kimanta arzikin da aka ce Mansa Musa ya mallaka, inda suke ganin ai babu wasu takamaiman alkalumma dake nuni ga yawan arzikin sa, a cewarsu, arzikin Mansa Musa ya wuce misali.
Don haka idan aka tambayeka ‘wanene attajirin daya fi arziki a tarihi?’ da fatan kasan amsar.