TASKAR BABAN SALMA

Babu wata al'uma ingantatta wadda bata da tarihin ta! daga Taskar Baban Salma

Sau 40 ba ayi Hajji ba a tarihi

Wallafan May 24, 2020. 1:08am. Na Abubakar A Gwanki. A Sashin Alajabi

http://zamaniweb.com/administrator/files/20/05/168/kaaba.jpg
SHIMFIDA
Hajji ibada ce daya daga cikin wajibai guda biyar ga musulmai. Kowacce shekara a watan musulunci na Zul-Hijja wata na 12 cikin jerin watannin musulunci. Musulmai daga ko ina a fadin duniyar nan kan tafi Birnin Makka na kasar Saudi Arabiya domin sauke faralin ibadar aikin Hajji. Ana bukatar kowanne musulmi mai iko ya yi wannan ibadar koda sau daya ne a rayuwar sa.
Shin ko kataba jin labarin cewa akwai wata shekara da musulmai suka tsallake ba tare da sunyi aikin Hajji ba? A sakamakon bazuwar annobar COVID-19 wadda ta sauya komi a duniya, musulmi a yanzu na fargabar yiyuwar dakatar da yin aikin Hajjin shekarar bana ta 2020. Tun da farko dama gwambatin kasar Saudi Arabiya ta rufe masallatai masu alfarma guda biyu na Makka da Madina wadanda dama a sune ake yin wannan ibadar ta aikin Hajji. Al'umar musulmai na ganin hakan a matsayin bakon al'amari a duniyar musulunci. Amma kuma saidai akasarin musulmai basu da masaniyar cewa sau 40 ana dakatar da ibadar aikin Hajji a tarihi, tun bayan wafatin Manzon Allah Annabi Muhammad (s.a.w).
An dakatar da aikin Hajji a lokuta da dama har sau 40, amma tun bayan kafuwar Daular Masarautar Saudi Arabiya ta yanzu, ba'a taba tsallake koda shekara daya ba. Koda annobar Spanish Flu da aka yi bata sa anki yin ibadar aikin Hajji ba.
GA BAYANIN NAN
629 AD:Lokacin farko da aka fara dakatar da Hajji
An taba dakatar da Hajji a shekarar 629 AD. Sakamakon kisan kiyashi da akayi a Dutsen Arfa.

865 AD: Kisa akan Dutsen Arfa
Rikici ne akayi tsakanin Ismail Bin Yousuf da Kalifan Daular Abbasiyya na Bagadaza sakamakon mummunan harin da aka kaishi a Dutsen Arfa a shekar 865 AD. Wannan ibtala'in yayi sanadiyyar rasa rayukan mutane da dama, kuma yayi sanadiyyar dakatar da aikin Hajjin shekarar.


[/b]
930-940 AD: Andakatar da Hajji har tsawon shekaru goma
A shekarar 930 AD, an dakatar da Hajji lokacin da Qarmatiyawa suka kai hari. Masana tarihi sunyi ikirarin cewar sojojin Abu Tahir sun hallaka mahajjata sama d 30,000 a Makka. Kuma aka saka gawarwakin cikin rijitar ZamZam. Faruwar haka ne ya sake haddasa yaki tsakanin Kalifofin daulolin Abbasid da Fatimid, kuma yayi sanadiyyar dakatar da Hajjin shekarar 983. Rikicin siyasar su yayi sanadiyyar hana aikin Hajji har na shekaru takwas har shekarar 991.
Sojojin Qarmatiyawa suka sace dutsen Hajrul Aswad. Sakamakon haka kuwa sai musulmai suka dakatar da yin ibadar Hajji har sai bayan da suka dawo da dutsen.

967 AD: An dakatar da Hajji sakamakon annoba
A shekar Hijira ta 357 (968 AD) wata annoba ta barke a garin makka wadda tayi sanadiyyar mutuwar dubban mutane da dabbobi. Haka yasa aka dakatar da yin aikin Hajjin shekarar.


983 – 991 AD: An dakatar da Hajji har shekara 8
Wani yakin tsakanin daulokin Abbasid da Fatimid ya sake barkewa kuma yasa ba'ayi Hajji ba a shekarar.
Abbasid na da iko da Iraki da Siriya yayin da Fatimid ke iko da Misira, suka hana Hajji har tsawon shekaru takwas.

1256 -1260 AD: Ba'ayi Hajji ba sabo da rigimar siyasa har na shekaru 5
Mutanen Hijaz, Said Arabiya ne kadai sukeyi Hajji a shekarun 1256 zuwa 1260


1831AD: An dakatar da Hajji sakamakon annoba
A shekarar 1831, annoba ta taso daga kasar Indiya inda taje har kasar Saudi Arabia. Annobar ta hallaka kaso uku cikin hudu na mahajjatan shekarar, kuma tasa ba'ayi aikin Hajji ba.

[p]1837 – 1858: Jerin annobobi

A cikin shekarunnan arba'in, ansamu jerin gwanan annobobi a garin Makka wadanda sukayi ta kawi tangarda tare ma da dakatar da Hajji baki data. A 1837, cutar amai da gudawa ta barke a Makka. Aka dakatar da Hajji har zuwa 1840. Sannan a 1846 annobar ta amai da gudawa ta sake barkewa a Makka a 1846 da wata kuma a 1858. Sai kuma wata annobar ta mutuwa a 1831. Sannan a karshe kuma an dakatar da Hajji a 1837 zuwa 1858.
[/p]

Wadannan bayanai ne da na samo su daga shafukan yanar gizo na tarihi. Saida nayi bincike maikyau na yarda da ingancin su sannan na zo na wallafa su a wannan shafin mai albarka. Nagode da karatu sosai -naku Abubakar A Gwanki (mai gudanarwa na shafin Taskar Baban Salama

Tura wannan zuwa:

Kasance na farko wajen yin sharhi a kan "Sau 40 ba ayi Hajji ba a tarihi"

Wallafa Sharhi

Suna:

Adireshin Email:

Sharhin:

Taskar Baban Salama, Taskar Tarihi

Barka da zuwa Taskar Baban SalmarnrnWannan dandali ne matattarar tarihi, wadda zata rinka kawo bayanai dangane da tarihi kan abubuwan da suka shude cikin harshen hausa. Abubakar A Gwanki ne babban mai gudanarwa a shafin. Kasantuwar sa mai sha'awa da tarihi ne kuma mai yawan karance karancen tarihi, shiyasa shima ya bude wannan farfajiyar domin samar da makaloli wadanda suka danganci tarihi cikin harshen Hausa.


Abubakar A Gwanki

Abubakar A Gwanki ne mai gudanarwa kuma mawallafin dukkannin abubuwan da wannan shafin ya kunsa.
Abubakar A Gwanki, masoyin tarihi ne sosai, kuma yana da sha'awar yin karance karance musamman na abubuwan da suka danganci tarihi.


Kasidu Masu Alaka