TASKAR BABAN SALMA

Babu wata al'uma ingantatta wadda bata da tarihin ta! daga Taskar Baban Salma

Sultan Moulay Ismail

Wallafan May 24, 2020. 7:58am. Na Abubakar A Gwanki. A Sashin Tarihin Mutane

http://zamaniweb.com/administrator/files/20/05/168/screenshot_2020-05-24-07-33-34-1.png
Wani marubuci dan Faransa Dominique Busnot cikin rubuce rubucen sa ya ce Moulay Ismaïl na Moroko yana da yaya 1,171. Koda littafin adana muhimman abubuwan tarihi na Guinness Book of World Records ya ce Sarkin na Moroko na da yaya 880. Ya kuma ce Sultan din nayin jima'i sau daya a kowacce rana saida yayi shekaru 32. Sultan Moulay Ismail muhimmi ne a cikin al'adu na kasar Moroko. Ya mulki kasar cikin iko da karfin mulki na sojoji sama da 150,000, mafi yawancin su bayi ne daga yankunan Saharar Afrika. Moulay Ismail ya sha saka mata a cikin sojojin kasar, kuma yayi amfani da kananan yara wajen gadi.
Amma ya ainahin hakikanin ikirarin cewar yana da yaya sama da 1000.

Sultan Moulay Ismail

Sultan Moulay Ismail na Moroco, ana kallon sa kamar wani makashi ko mashayin jinin jama'ar sa, shine nabiyu cikin sarakunan ahalin gidan sarautar Alaourite kuma yayi sarautar Morok tsakanin 1672-1727. Asalin sa dane ga bayi bakaken fata, amma yayi ikirarin cewa shi daga ahalin Mazon Allah Annabi Muhammad (s.a.w) yake. An kuma aiyana shi da sarki mafi karfin iko a Moroko.

Bayan rasuwar sarki Saadi Sultan Ahmad al-Mansur, Moroko ta shiga cikin hargitsi, lokacinne yayan sarkin suka dunga yaki a tsakanin su domin neman sarauta. Hakane ya raba kan kasar inda aka samu masarautu daban daban a kasar. Daga baya wasu sarakuna daga yan'uwan Moulay sai suka janye masarautun su suka mika masa mulki.

Ana kallon sa mutum mai yawan zubar da Jini

Anyi kiyasin cewa Moulay ya kashe sama da mutane 30,000 banda wadanda suka rasa rayukan su a filin daga. Hakanan, a kokarin sa na kare matan sa guda hudu da kwarkwarorin sa 500, kowanne mutun aka samu da laifin ya kalli daya daga cikin matan sa hudu ko kwarkwarorin sa 500 to hukuncin kisa ya hau kansa. Hakanan duk wata mata da bata daga cikin matansa ko kwarkwarorin sa, idan ta kalli sarkin cikin yanayi na nuna sha'awa gareshi to ana yanke mata mama ko kuma a cire mata hakora.

Maganganu kan yayan sa


Akwai maganganu da suka tabbatar da cewa Sultan Moulay Ismail yana da yaya sama da 1000 ko dai kusa da haka. daga ciki akwai kundin adana muhimman abubuwan tarihi na "Guinness Book of World Records", Iyace smaïl yana da yaya 888, kuma shine yafi kowa yaya a duniya. Hakanan daga cikin kundin rubutun ambassadan faransa a Moroko Dominique Busnot, yace a shekarar 1704, Ismail na da yaya 1,171. A wannan lokacin Ismail nada shekaru 57 da haihuwa kuma yana da shekaru 32 a kan karagar mulki.

Saidai da fatko masana kimiyya suna da ja kan cewa ko mutum zai iya haifar wadannan yayan a rayuwar sa. Amma a wani bincike da kididdigar kimiyya da aka fitar yace, mutum yana da yawan mata haka, kuma yana saduwa da kowacce a rana har ya kwashe shekaru 32 to zai iya haifar wadannan yayan. Shi kuwa Sultan Ismail nada wadatar mata, kuma yanada da damar yin jima'i a kowanne lokaci yaso.

Moulay Ismail yayi sarautar Moroko na tsawon shekaru 55, kuma ya rasu a 22 ga Maris, 1727. Shekarun sa 81. Har yau ba'ayi sarkin da ya kaishi dadewa ba a karagar mulkin sarautar Moroko.

Tura wannan zuwa:

Kasance na farko wajen yin sharhi a kan "Sultan Moulay Ismail"

Wallafa Sharhi

Suna:

Adireshin Email:

Sharhin:

Taskar Baban Salama, Taskar Tarihi

Barka da zuwa Taskar Baban SalmarnrnWannan dandali ne matattarar tarihi, wadda zata rinka kawo bayanai dangane da tarihi kan abubuwan da suka shude cikin harshen hausa. Abubakar A Gwanki ne babban mai gudanarwa a shafin. Kasantuwar sa mai sha'awa da tarihi ne kuma mai yawan karance karancen tarihi, shiyasa shima ya bude wannan farfajiyar domin samar da makaloli wadanda suka danganci tarihi cikin harshen Hausa.


Abubakar A Gwanki

Abubakar A Gwanki ne mai gudanarwa kuma mawallafin dukkannin abubuwan da wannan shafin ya kunsa.
Abubakar A Gwanki, masoyin tarihi ne sosai, kuma yana da sha'awar yin karance karance musamman na abubuwan da suka danganci tarihi.


Kasidu Masu Alaka

  • [Hoto] Game da shafi
    Assalam Alaikum, barka da zuwa wannan shafin. A wannan shafin na Taskar Baban Salma, zamu rinka kawo maku makaloli masu nasaba da tarihi. Idan kai ...Budo cikakke
  • Hoto Abubuwan da suka sauya duniya
    Kasan tuwar ka dan adam, shin ka tabayin tunani dangane da ya duniya take a shekarun da akecema BC wato (Kafin haihuwar Annabi Isah)? Shin da ace a du...Budo cikakke
  • [Hoto] Teku mafi girma a duniya
    Tekun Pacific ita ce Teku ma fi girma a wannan Duniya ta mu , domin kuwa Tekun ta pacific ta kwashe fiye da kashi 45 bisa dari na yawan tekun da ke ...Budo cikakke