TASKAR BABAN SALMA

Babu wata al'uma ingantatta wadda bata da tarihin ta! daga Taskar Baban Salma

Wasu abubuwa daya kamata ku sani akan shugabannin Najeriya

Wallafan July 22, 2020. 12:54pm. Na Abubakar A Gwanki. A Sashin Tarihin Mutane

http://zamaniweb.com/administrator/files/20/07/168/tmp-cam-828658661.jpg

Wann irin sani kayi shugabannin Najeriya? Wanene wanda ya kirkiri babban bankin kasar? Ko kasan cewa tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo baisa takalma ba a shagalin bikin auren matarsa ta farko? Kana son kasan jihar da tafi fitar da shugabannin kasa zababbu? To ka karanta wannan makalar...
1. Har kawo wannan rubutun da nake yi, ba'a taba yin shugaban kasa ba a Najeriya wanda aka haifa bayan shekarar samaun yancin kai ta 1960.
2. Haryanzu babu tabbacin ranar haihuwar tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo. Amma yana amfani da 5 Maris, 1938 a matsayin ranar haihuwar sa. Kuma bai saka takalma ba a shagalin bikin sa da matar sa ta farko Remi. Kuma shine kadai shugaban kasar da matar sa ta mutu yana kan mulki wato marigayiya Stella, Oktoba 2005.
3. Tsofaffin shugabannin kasa Obasanjo da Goodluck Ebele Jonathan sune kadai mataimakan shugaban kasa wadanda suka maye gurbin shugaban kasa bayan mutuwar su. Ranar 14, Fabrairu 1976, bayan kisan gillar da aka yima Murtala Muhammad Obasanjo ya maye gurbin sa sannan Jonathan ya maye gurbin Umaru Musa Yar'adua bayan rasuwar ranar 6 Mayu, 2010.
4. Obasanjo da Muhammadu Buhari sune kadai shugabannin da suka muki Najeriya a mulkin soja da na farar hula. Obasanjo yayi mulkin soja daga 14 Fabrairu 1976, zuwa 30 Satumba, 1979, dakuma na farar hula daga 29 Mayu, 1999, zuwa 29 Mayu, 2007, sannan Buhari yayi mulkin soja daga are 31 Disamba, 1983, zuwa 26 Ogas, 1985, sai yayi na farar hula daga 29 Mayu, 2015 zuwa yau.
5. Dukkan shugabanni biyun da suka gaji Obasanjo a mulkin sa na soja a 1979 da na farar hula a 2007basu kammala zangon mulkin su ba. Amma Shehu Shagari juyin mulki a hawansa na biyu ranar 31 Disamba, 1983, sannan Yar'adua ma ya rasu yana tsakiyar zangon sa na farko a 2010.

6. Su wadannnan shugabannin wato Shagari da Yar'adua dukkan su sunfito ne daga yankin Arewa maso yammacin Najeriya, dukkan su fulani ne, kuma dukkan su Musulmai ne, sannan dukkan su malaman makaranta ne.

7. Yayin da jinin sojojin kasar yake zuba a tsakiya da yakin basasar Najeriya ne, Shugaba Yakubi Gowon ya angwance da matar sa Victoria Zakaria. Gowon kuma shine kadai shugaban Najeriya mai ilimin digiri matakin bachelor kuma mafi kankantar shekaru da yahau kan mulki yana da shekaru 31 da kwana 288, kuma na farko da yayi aure yana kan mulki. Kuma Gowon yayi shekaru 9 yana mulki, mafi dadewar shekaru a jere akan mulkin Najeriya da wani shugaba ya tabayi.

8. An kashe Sir Ahmadu Bello da matarsa a 1966 lokacin Major Kaduna Nzeogwu ya shirya juyin mulki. Kakan sa Uthman Dan Fodio shine wanda ya kafa daular Fulani a Arewacin Najeriya. Babbar jami'a a yammacin Afrika kuma ta biyu a nahiyar Afrika an saka mata sunan shi.


9. Chief Ernest Shonekan da Olusegun Obasanjo sune kadai shugabannin Najeriya daga yankin yammacin kasar. Dukkan su kuma yan garin Abeokuta ne na jihar Ogun. Kuma kukkan su Kiristoci me.

10. Mutumin dake jikin takardar Naira 10 Alvan Ikoku da dansa Samuel Goomsu Ikoku yan adawar siyasa ne. Samuel ya taba kayar da mahaifin sa a wani zabe na yan majalisu a yankin gabashin Najeriya Maris 16, 1957.

11. Sir Abubakar Tafawa Balewa bai cancanci zama firayiministan Najeriya ba a 1959, amma Ahmadu Bello lokacin yana matsayin shugaban jam'iyyar Northern People’s Congress, NPC ya damka masa ragamar ya tura shi Lagos.

12. Mutumin dake jikin kudin Najriya Naira daya, Herbert Heelas Olayinka Badmus Macaulay shine Injiniya na farko a Najeriya, kuma shine ya fara kafa jam'iyyar siyasa a Najeriya. Mahaifiyar sa Abigail, diya ce ga Bishop Samuel Ajayi Crowther kuma mahaifin Macaulay shine Thomas Babington Macaulay, wanda shine ya fara kafa makarantar sakandire a Najeriya. Hallau dai Macaulay magaji ne gaStella Ameyoh Adadevoh, matar da ta dakatar da annobar Ebola.

13. General Murtala Mohammed da General Sani Abacha dukkan su anhaife su kuma an binne su a Kano.

14. A matsayin shugaban kasar Najeriya, Murtala Mohammed yana yawo ne shi kadai ba tare da jami'an tsaro ba. Shine kadai shugaban Najeriya da ya rasu bai kai shekaru 40 ba, ya rasu yana da shekaru ranat 13 Fabrairu 1976, bayan harbin sa da akayi a yayin yi masa juyin mulki. Yana da shekaru 37.

15. Anhaifi General Sani Abacha ranar Litinin 20 Satumba, 1943, kuma ya rasu ranar Litinin, 8 Yini, 1998.

16. Jihohin Niger, Katsina, da Ogun su sukafi samar da shugabannin kadar Najeriya.


17. Umar Musa Yar’Adua shine kadai zababben shugaban kasa wanda ya rasu a ofis.


18. Lokaci yakin basasa, shugaban Biafra Chukwuemeka Odumegwu Ojukwu da takalma yake barci abin sa.


19. Major-General Johnson Thomas Umunakwe Aguiyi-Ironsi shine shugaban soji na farko a Najeriya. Kuma ya shiga aikin soja dana da shekaru 18 kadai.

20. Chief Festus Okotie-Eboh shine ya kirkiri babban bankin Najeriya a 1959 lokacin yana ministan harkokin kudi. Shine kadai minista a cikin wadanda aka kashe a lokacin juyin mulkin 1966.


21. Kiristoci sun mulki Najeriya na tsawon shekaru 25 da wata 9, yayin da Musulmai suka shugabanci Najeriya na tsawon shekaru 34 da wata 11. Shugaban Najeriya mai ci yanzu musulmi be, shine Muhammadu Buhari.


22. Chief Ernest Adegunle Oladeinde Shine kadai farar hula wanda ya shugabanci kasa kuma ba tare da jam'iyyar siyasa ba. Kuma shine kadai wanda ba'a zaba ba, kuma shi kadai ne wanda yayi murabus daga shugabancin kas ranar 17 Nuwamba, 1993.


23. Shonekan, shine mafi karancin dadewa a wadanda suka shugabnci Najeriya, yayi mulki ne kawai n watanni 2 da kwana 21 yayin da Olusegun Obasanjo yayi shugabanci na soja da farar hila na tsawon shekaru 11 da kwana 228, hakanne yasa shine mafi dogon shugabancin Najeriya.


24. Dukkan shugaban mulkin soja na Najeriya mai mataimaki dan jihar Ogun to a ofishi ya rasu.


25. Dukkannin shugabannin Najeriya na farar hula to tsofaffin malaman makaranta ne a baya, banda Olusegun Obasanjo da Muhammadu Buhari.


26.Babu jihar da ta samar da shugabannin kasa a Najeriya kamar jihohin Niger, ( Ibrahim Babangida , Abdussallam Abubakar), Katsina (Muhammadu Buhari, Umar Musa Yar’Adua), da Ogun (Olusegun Obasanjo, Ernest Shonekan).
Ojukwu ya koya wa Murtala Mohammed aikin soja a Teshie, Ghana. Dalibin ya yaki malamin sa a lokacin yakin basasa.


27. a 1966, Najeriya ta zama bata da shugaba na tsawon kwanaki 3 (29 Yuli, - 1 Ogas).


28. Chief Samuel Ladoke Akintola (1910-1966) shine ya fara kawo mota mai sulke Najeriya a 1964. Akan kudi yuro £8000 mota samfurin Mercedes Benz.


29. President Goodluck Ebele Jonathan ne shugaban kasa daya tilo da yasha kaye a zabe yayin neman wa'adin mulki na 2 a 2015


30. Shugabannin kasa da suka iya manyan harsunan kasar uku (Hausa, Igbo, da Yoruba) sosai yan kabilar Ibo ne; Nnamdi Azikiwe da Johnson Thomas Aguiyi-Ironsi.

........
Idan kaji dadin wannan makalar ko kuma kana da gyara to kana iya aiko mana ta akwatin sharshi dake kasa.

daga marubuci Abubakar A Gwanki

Tura wannan zuwa:

Kasance na farko wajen yin sharhi a kan "Wasu abubuwa daya kamata ku sani akan shugabannin Najeriya"

Wallafa Sharhi

Suna:

Adireshin Email:

Sharhin:

Taskar Baban Salama, Taskar Tarihi

Barka da zuwa Taskar Baban SalmarnrnWannan dandali ne matattarar tarihi, wadda zata rinka kawo bayanai dangane da tarihi kan abubuwan da suka shude cikin harshen hausa. Abubakar A Gwanki ne babban mai gudanarwa a shafin. Kasantuwar sa mai sha'awa da tarihi ne kuma mai yawan karance karancen tarihi, shiyasa shima ya bude wannan farfajiyar domin samar da makaloli wadanda suka danganci tarihi cikin harshen Hausa.


Abubakar A Gwanki

Abubakar A Gwanki ne mai gudanarwa kuma mawallafin dukkannin abubuwan da wannan shafin ya kunsa.
Abubakar A Gwanki, masoyin tarihi ne sosai, kuma yana da sha'awar yin karance karance musamman na abubuwan da suka danganci tarihi.


Kasidu Masu Alaka